page 59

1.7K 116 4
                                    

*🌹🌹 DEEDAT🌹🌹*

*Writing by RASHIDA USMAN*

*Wattpad*

*rashmarrka*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 59

Momy ai hakuri yazama dole dan narasa shi kenan har abada tunda zuciyarsa na wani guri.  To kita addu'a Allah ya kawomaki wani mai albarka amma wanan  tunanin da kikeyi bayada amfani.

Kuka ta fashe da shi tace wallahi Dady ya cuce ni yanzu wa zai aure ni a haka?

Dafata momy tayi tace kibar ma Allah komai yana sane da duk halin da kike ciki kuma kiyi tawakkali da Allah ne ya ƙaddara maki komai sai kiga haske a al'amarin ki.

Rungume momy tayi tace nagode sosai Allah ya barmin ke my sweet momy.

Bata ce mata komai ba sai murmushi takeyi mai ciwo tana shafa bayan ta, sun ɗauki lokaci a haka.

Sati biyu ya rage bikin Sa'imah da Deedat, shirye _shirye ake ba kama hanun yaro ta kowane ɓangare shiri sukeyi, mutanen Dubai da Niger sun fara hallara,   duk wata haidima dasu akeyin ta lokaci yana ta kawo jiki, ranar da su Gwaggo zasu zo ita da su Abdallah shiri akeyi na musamman, sai gyaran gida akeyi, sai yamma liss suka sauka, sosai Abdallah  ya tausawa masu yana ganin ace yana da rai ace wai ƴan uwansa suna cikin wanan rayuwar ta halin babu, ɗaki na musamman aka gyara masa, kwanan sa biyu da zuwa ya nemi Gwaggo ya gaya mata shawarar da ya yanke na son Innah ta tattara sukoma Abuja ayi biki acan dan a ganin sa wanan gidan yayi masu ƙarami.

Da Gwaggo ta faɗa ma Innah dafari taƙi yarda saida yayi mata bayanin cewa ko rabin ƴan uwan su da suka ɗauki alƙawarin zuwa wanan gidan bazai ɗauke su ba, sanan ta amince.

Taɓan garen Sa'imah kuwa tana shan gyara na musamman dan ɗaya daga cikin ƴan uwan su na Dubai ita take mata gyaran jiki, saida aka fara  bata magunguna infection da na basir sanan aka fara bata maganin mata, Sarah kuwa tun biki na saura wata ɗaya ta dawo gidan, da ita ake komai, mamy ma kusan kullum tana gidan, lokacin da ta bama Abdallah  labarin itace ta taimake su yayi mata kyauta mai tarin yawa saida tayi hawaye jin daɗi.

Saura kwana biyu su koma Abuja, tana kwance a ɗaki waya takeyi da Deedat, take gaya masa ga abin da kakanta ya yanke na komawar su Abuja yayi masu murna sosai kuma yaji daɗin haka dan Abubuwan zasu masa sauƙin zirga-zirga.

Falo Innah ta fito domin kiran Gwaggo, can ta ganta tana fira da ɗaya daga cikin baƙin da suka zo daga Dubai magana tayi mata akan ta taso tana son tayi   magana da ita, tashi tayi ta nufi ɗakin Innah saida ta zauna sanan tace inajin ki.

Dama cewa nayi yakamata a gayama su Hamma Aminu maganar bikin ya matso, da kuma tashimu a wanan garin.

Karki damu yanzu haka an tura motaci su ɗauko su sai mu tafi ga baki ɗaya ai yafi sauƙi.

Gwaggo dama inaso na bama Maman Sarah wanan gidan.  To A'isha ni bazan hanaki kyauta ba amma kiduba wanan yaron da yabaki shi bazai ji daɗi ba idan yaga kinyi kyauta dashi, sai ya ga kamar dan kinyi kuɗi ne yanzu yasa kika bayar da shi.

To bara kawai na siya mata wani na bata dan gaskiya tayimin taimakon da har na mutu bazan manta da ita ba.

Da kin kyauta kuwa bari akwai wasu kuɗi da na dawo da su sai nabaki ki haɗa ki siya mata. To Nagode Gwaggo na.

DEEDATWhere stories live. Discover now